Acts 13

An Aiki Barnabas da Shawul

1A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai: Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawul. 2Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawul domin aikin da na kira su.” 3Saboda haka bayan suka yi azumi da adduʼa, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.

A Saifurus

4Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus. 5Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majamiʼun Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu.

6Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani Bayahude mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu, 7wanda yake maʼaikacin muƙaddas Sergiyus Faulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawul domin yana so ya ji maganar Allah. 8Amma Elimas mai sihirin nan, (domin maʼanar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya. 9Sai Shawul, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce, 10“Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba? 11Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.”

Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora.
12Saʼad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.

A Antiyok na Fisidiya

13Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a jirgin ruwa zuwa Ferga a Famfiliya inda Yohanna ya bar su ya koma Urushalima. 14Daga Ferga kuwa suka ci gaba zuwa Antiyok na Fisidiya. A ranar Asabbaci sai suka shiga majamiʼa suka zauna. 15Bayan an yi karatu daga cikin Doka, da kuma Annabawa, sai shugabannin majamiʼar suka aika musu suka ce, “ʼYanʼuwa, in kuna da wani saƙon ƙarfafawa domin jamaʼa, sai ku yi.”

16Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce: “Mutanen Israʼila da kuma ku Alʼummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni! 17Allahn mutanen Israʼila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar, 18ya kuma jure da halinsu har shekara arbaʼin a cikin hamada, 19ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kanʼana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa. 20Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450.

“Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Samaʼila.
21Saʼan nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawul ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arbaʼin. 22Bayan an kau da Shawul, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa: ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’

23“Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Israʼila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari. 24Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi waʼazin tuba da baftisma ga dukan mutanen Israʼila. 25Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce: ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. Aʼa, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’

26“Ya ku ʼyanʼuwa, ʼyaʼyan Ibrahim, da ku kuma Alʼummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto. 27Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci. 28Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yǎ sa a kashe shi. 29Saʼad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari. 30Amma Allah ya tashe shi daga matattu, 31kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu.

32“Muna gaya muku labari mai daɗi cewa: Abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari, 33ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin ta da Yesu daga matattu. Kamar kuma yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa,

“ ‘Kai Ɗana ne,
yau na zama Uba a gare ka.’
Zab 2.7

34Gaskiyar cewa Allah ya ta da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi:

“ ‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’
Ish 55.3

35Haka kuma aka faɗa a wani wuri:

“ ‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’
Zab 16.10

36“Gama saʼad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe. 37Amma wanda Allah ya ta da daga matattu bai ruɓa ba.

38“Saboda haka, ʼyanʼuwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi. 39Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba ta iya kuɓutar ba. 40Ku lura kada abubuwan da annabawa suka faɗa su faru muku:

41“ ‘Ku duba, ku masu baʼa,
ku yi mamaki, ku hallaka,
gama zan yi wani abu a zamaninku
da ba za ku taɓa gaskatawa ba
ko da wani ya gaya muku.’
Hab 1.5

42Bulus da Barnabas suna fita daga majamiʼar ke nan, sai mutane suka gayyace su su ƙara yin maganan nan a kan waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci mai zuwa. 43Da aka sallami jamaʼa, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah.

44A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji. 45Saʼad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi.

46Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagaɗi: suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Alʼummai. 47Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa:

“ ‘Na sa ka zama haske ga Alʼummai,
domin ka kawo ceto har zuwa iyakar duniya.’
Ish 49.6

48Saʼad da Alʼummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata.

49Maganar Ubangiji kuwa ta bazu a dukan yankin. 50Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka ta da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu. 51Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum. 52Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.

Copyright information for HauSRK